Ya Musawwir! Kai Mana Mafita, Ka Dafa mana,Ka kawo mana saukin dukkan Abunda Yafi Karfinmu. Ka Sada Mu Da Rahamarka, Kajiqan Magabatanmu. Alfarmar Annabin Rahma S. A. W. Barkanmu da Safiyar Laraba
Ya ALLAHU Ka Tsare Mana imaninmu, Ka Tsarkake Mana niyyarmu, Ka Ciyar Damu Daga Taskarka, Ka shiryemu Da Zuriyarmu, Kajiqan Dukkan magabatanmu. Alfarmar Annabin Rahma S. A. W. Barkanmu da Safiyar Talata
Ya Ubangiji Kayi Gafara, Garemu Da Dukkan magabatanmu, Ka Shafe Dukkan Zunubanmu, kasanya Mu Cikin Ludufinka, Shiryar Damu Da Zuriyarmu. Alfarmar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam. Barkanmu da Safiyar Litinin
Ya Ubangiji kasanya Mu Cikin Bayinka Masu sada zumunci, Yin Uzuri, Yafiya, Neman Yardarka, Gafararka,Zikirinka Da Aminchewarka, Ka Sada Mu Da Dukkan Alkhairin ka. Alfarmar Annabi S. A. W. Barkanmu da Safiyar Lahadi
Ya ALLAH Kayi Aminchi Damu, Da Ayyukanmu, Ka shiryar Damu da Zuriyarmu, Kasanya Mu cika Da Imani Ka bamu ikon tashi dashi, Ka Shafe Zunubanmu Dana magabatanmu. Alfarmar Annabin Rahma S. A. W. Barkanmu da Safiyar Asabar
Ya Azeez ! Muna Neman Yardarka, Gafararka, Rahamarka, Tsarkake Zuriyarmu, Ka Azurtamu Da wadatar zuci, Kagafartawa Magabatanmu. Alfarmar Annabin Rahma. S. A. W. Barkanmu da Safiyar Juma’at
Ya Wahab !Ka Saukar Da Ni’imarka Garemu, Ka jaddada Rahma, Ka Haskaka, Makwancin Dukkan Magabatanmu, Kayi Mana kyakyawan karshe, Kayi Mana Mafita. Alfarmar Annabin Rahma S. A.W. Barkanmu da safiyar Alhamis
Ya Hakeem ! Ka Kubutar Damu Daga Tsawon Buri, Son Zuciya, Barin Gaskiya, Aikata Dukkan Nau’in Sabonka, Ka Shafe Dukkan Zunubanmu, Kajiqan Dukkan magabatanmu. Alfarmar Annabin Rahma S. A. W.Barkanmu da Safiyar Laraba
Ya zuljalal Wal Ikram! Ka Yaye mana Wannan Musiba, Ka karfafa Rauninmu, Ka Karya Munafukan cikinmu, Ka Bamu ikon tashi mu yaqi dukkan Azzalumai da zaluncin shuwagabanninmu, Alfarmar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam. Barkanmu da Safiyar Talata
Ya Sami’u, Ya mujibu! Ka kawo mana taimakonka akan Dukkannin Azzalumai da zalunci, ka Karya masu Haddasa , Assasasa, Tallafawa da Aikata Wannan Ta’addanci a Wannan kasa. Alfarmar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam. Barkanmu da Safiyar Litinin