MUHADARA KAN HUKUNCE-HUKUNCEN AZUMI:
*MAI GABATARWA: Dr. Kabiru Adamu Lamido Gora
*RANA: Yau Lahadi 15/2/2026
*LOKACI: Bayan Sallar Magariba.
*WURI: Masallacin Bin Baz, G.R.A Jalingo.
Allah ya bada ikon halarta, amin
GIRMAN LADAN MATAR DA 'YA'YANTA SUKA RASU
Daga Abu Sa’id Al-Khudri (R.A) cewa Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Duk Matar da ‘ya’yanta guda uku suka rasu, za su zama katanga a gare ta daga wuta." Sai wata mata ta ce: " idan biyu ne fa?" Sai ya ce: "Har da biyu."
Bukhari da Muslim.
UMARNIN NEMAN ARZIKI NA HALAL
Daga Jabir dan Abdullahi, Allah ya kara masa yarda,
Manzon Allah (ﷺ) ya ce : "ku ji tsoron Allah, ku kyautata wajen nema, ku sani wata rai ba za ta taba mutuwa ba har sai ta cika arzikin ta da aka rubuta mata."
Ibn majah.
WADANDA ALLAH YAKE SO, SU YAKE JARRABA
Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "idan Allah ya so mutane to sai ya jarrabe su, duk wanda ya yi hakuri to zai sami ladan Hakurin, duk wanda ya yi raki to zai sami zunubi na rashin hakurin."
Imam Ahmad.
Assalamu Alaikum
His Eminence, the Sultan of Sokoto has declared Monday 22/12/2025 as the first day of Rajab 1447 AH.
Yahaya Muhammad Boyi
Sarkin Malaman Sokoto
Sahih Muslim.
*Karin bayani:
Wajibi ne ga duk wanda Allah ya bashi shugabanci, ya tausayawa wadanda yake shugabanta, ya basu kulawa, ya yi iya yinsa wajan ganin halinsu ya gyaru, kuma ya kiyayi tsananta musu.
ADDU'A GA SHUGABANNI MASU TSANANI DA MASU TAUSAYI
Manzon Allah (ﷺ) ya ce: Ya Ubangiji, duk wanda ya jibinci lamarin wani abu na al'umata sai ya tsananta musu, shi ma ka tsananta masa, duk wanda ya jibinci lamarin wani abu na al'umata, sai ya tausaya musu, shi ma ka tausaya masa
HANIN YADA SIRRIN JUNA GA MA'AURATA
Daga Abu Sai'd Alkhudri, (R.A), Manzon Allah (ﷺ) ya ce :*"Lalle yana daga mafi sharrin mutane a wajen Allah, a ranar Alkiyama, Mutum ya biya bukatarsa da matarsa, ta biya bukatarta da shi, sannan ya zo ya rika yada sirrinta."
Imam Muslim.
ƘWAƊAITARWA AKAN KYAUTATAWA MAƘWABCI
Daga Abu Hurairah, Allah Ya ƙara masa yarda, Manzon Allah ﷺ ya ce: "Ya ku mata musulmai, kada wata maƙociya ta raina abinda za ta bawa maƙociyarta komai kankantarsa, ko da daidai da kofaton akuya ne, (ko kashi mai romo)."
Bukhari da Muslim