Under ALLAH's protection,may we live in good health,abundant wealth,peace,and love,May our paths be guided,our burdens lifted,and our prayers answered,may living,learnin,and succeeding be easy for us.
Ameen Ya Rabb 🤲🤍
Daga Miƙdam (R) Manzon Allah (S) ya ce: ((Wani bai ci abinci mafi alkairi fiye da wanda ya samu ta hanyar aikin hannunsa ba. Lalle Annabin Allah Dawud ba ya ci sai daga aikin hannunsa))
📚 Bukhári
Daga Abú-Huraira (R) : Manzon Allah (S) ya ce: ((Mala'iku suna yin salati ga ɗayanku,matuƙar yana zaune a wajen da ya yi Salla,kuma bai yi hadasi ba; Suna cewa: Ya Allah ka gafarta ma sa ka ji ƙansa))
📚 Bukhári da Muslim
Manzon Allah (S) ya ce: ((Lalle ɗayanku ya yo tarin itace a gadon bayansa,shi ya fi ma sa alkairi a kan ya roƙi wani,ya ba shi ko ya hana shi))
📚 Bukhari da Muslim
Manzon Allah (S) ya ce: ((Duk wanda ya ga mummunan abu daga cikinku ya gyara shi da hannunsa,idan ba zai iya ba sai ya gyara da harshensa,idan ba zai iya ba sai ya ƙi abin da zuciyarsa; Wannan shi ne mafi raunin Imani))
📚 Muslim
Manzon Allah (S) ya ce: ((Babu wani bawa da zai yi raka'a goma sha biyu ta sallar nafila ba farilla ba,a yini,don Allah,face; Allah ya gina ma sa gida a Aljanna))
📚 Muslim
Daga Miƙdam (R) Manzon Allah (S) ya ce: ((Wani bai ci abinci mafi alkairi fiye da wanda ya samu ta hanyar aikin hannunsa ba. Lalle Annabin Allah Dawud ba ya ci sai daga aikin hannunsa))
📚 Bukhári
Daga Ibnu-Mas'ud (R) : Manzon Allah (S) ya ce: ((Farkon abinda za a yi wa bayi hukunci a kansa a ranar Alƙiyama shi ne Jini)). 📚Bukhari
Ma'ana: Shari'o'i da suka shafi kisan kai.*