HE STOOD FOR US WHEN IT MATTERED MOST.
Mallam Nasir El-Rufai is truly our comfort in times of tears. May Allah bless him with long life, protection, and strength. Ameen.
Sabuntawa/Update: Ranar 6 ga Afrilu, 2026
Na sanar da wani shiri na samar da allurai (syringes) da kayayyakin likitanci kyauta a dukkanin cibiyoyin lafiya na matakin farko (PHCs) da ke mazabar Kaduna ta Arewa. Wannan shiri yana tare da hadin gwiwar wani kamfani na gida mai dogaro da kai da kirkire-kirkire, Medical Plastics Limited.
Ina farin cikin sanar da cewa an riga an yi oda kuma za su iso Kaduna nan da gobe. Bayan haka, zan sanar da kwamitin wucin gadi da aka dora wa alhakin raba kayayyakin a dukkanin cibiyoyin lafiya na Shaba, Gaji, Maiburuji, Unguwar Liman, Gabasawa/Unguwar Rimi, Unguwar Sarki, Badarawa, Kabala, Unguwar Dosa, Kawo, Unguwar Shanu/Abakwa, da Unguwar Kanawa/Hayin Banki.
Kwamitin wucin gadi, tare da hadin gwiwar shugabannin PHCs, dattawa, da shugabannin gargajiya, dole ne su tabbatar da cewa al'umma sun amfana da wannan ba tare da biyan ko sisi ba. Wannan shi ne kadai bukatarmu kuma za mu sa ido wajen ganin an cika hakan.
Za mu ci gaba da hadin gwiwa da mutane, kamfanoni, da kungiyoyi masu hangen nesa don amfanin mutanen mazabar Kaduna ta Arewa. Godiya ta musamman ga dan uwana, Amir Baba Kusa. Allah SWT ya saka masa da alheri da iyalinsa baki daya. Kaduna ta Arewa ba za ta taba mantawa da wannan nuna tausayi ba.
Samun ingantaccen ilimi da lafiya masu saukin kudi sun kasance babban bangare na yakin neman zabena kuma su ne ginshikin ajandar dokata.
Sanya hannu/Signed
Hon. Mohammed Bello El-Rufai
Dan Majalisa, Mazabar Kaduna ta Arewa.
Shugaban Kwamitin Kula da Bankuna.
Afrilu 16, 2026.
Yesterday evening, I received stakeholders of the Adamawa State chapter of the ADC at my Abuja residence, a visit that deeply touched me. I thanked them for the gesture and reminded the new state leadership that unity is now their sacred duty: to heal divisions, carry everyone along, and lead with fairness. I remain convinced that the ADC has risen as Nigeria’s true opposition force. One that is strong in ideals, structure, and resolve, and ready to challenge and defeat the failing APC in the elections ahead. -AA