Red blood of royalty runs through my veins, a true born son of my royal fathers, I am very humble to be a descendant of the majestic royal house of Hadejia kingdom your proud and humble son is loyal ๐
๐จ BREAKING: Josรฉ Mourinho back to Real Madrid, HERE WE GO! ๐ฃ๐ค
All terms have been verbally agreed between Josรฉ Mourinho and Real Madrid, waiting to sign all documents.
Plan for initial two year deal, JM to travel to Madrid after Real-Bilbao game.
The Special One is back.
Mai Martaba sarkin Hadejia Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje CON bisa umarnin Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi na umartar Al'ummar musulmai da Gobe Laraba 18th February, 2026 za a tashi da Azumin watan Ramadan.
Allah ya amsa ibadun mu na wannan wata mai Albarka๐
13/02/2026 โ Shekara Biyar (5) da rasuwar Kakar Mu Hajja (Mai Babban Daki), Mahaifiya ga Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje, CON.
Muna adduโa Allah Ubangiji Ya gafarta mata, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarta, Ya sa kabarinta ya zamo haske da yalwa.
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje CON, ya halarci Taron Waโazin Kafin Ramadan na Shekarar 2026 da Jamaโatu Nasril Islam (JNI) ta gudanar a Hedkwatarta ta ฦasa da ke Kaduna, a ranar Lahadi, 2 ga Shaโaban 1447AH (8 Fabrairu 2026).
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, ya karษi bakuncin Sarkin Kaltungo, Engr. Saleh Muhammad Umar, OON, Ziyarar ta biyo bayan isar da godiya a madadin alโummar Kaltungo, bisa amsa gayyatar kasancewa Uban Taro a bikin baje kolin Alโadu na 2025.
Mai Martaba Sarkin Hadejia Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje CON ya halarci Lakca ta Farko da aka shirya don Girmama Marigayi Martaba Sarkin Dutse Alh. (Dr.) Nuhu Muhammad Sanusi, CON, wadda Kwamishinan Yaษa Labarai na Jihar Jigawa Hon. Sagiru Musa Ahmed ya shiryata.
His Royal Highness, the Emir of Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, paid a courtesy visit to the Emir of Machina, Alhaji Bashir Albishir Mai Machinama, during the Machina Annual Cultural Festival (MACUF 2026), which took place from 27th January to 1st February 2026.
Maimartaba Sarkin Hadejia Alhaji (Dr) Adamu Abubakar Maje CON ya halarci saukar karatun Al-qur'ani mai girma ta matan aure guda 13 a makarantar Alfijir International college Hadejia dake Unguwar Nasarawa cikin garin Hadejia.
Allah ya karawa Sarki Lafiya Ameen ๐
Asabar 24/1/2026
Say your prayers for my lovely little cousin sister Asma'u who passed away yesterday
Whenever Iโm on a call with her mom, she always asks, โYaya Baffa, Yaushe zaka dawo mu tafi Abuja tare, Tom Allah ya bada sa'a, adawo lafiya'
Allah ya jikan ta da Rahama yasa mai ceto ce๐
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje CON, ya halarci bikin kaddamar da shirin tallafawa alโumma da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya rabawa masu cin gajiyar shirin motocin sarauta, kayan noma, injinan zamani da sauran muhimman kayayyaki.
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje CON, ya halarci taron haษin gwiwa na Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya,Taron ya mayar da hankali kan tattaunawa kan matsalolin tsaro da ke addabar yankin wanda aka gudanar da shi a fadar gwamnatin Kaduna.
01.12.2025
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, ya halarci bikin cikar shekaru 45 na Mai Martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmad Muhammed Sani II, a gadon sarautar tare da kaddamar da Sabon Masallacin Jumaโa na Gumel da ke Karamar Hukumar Gumel a Jihar Jigawa.
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, Shugaban Majalissar Sarakunan jihar Jigawa ya halarci bikin dabar cikar shekaru 45 ta Mai Martaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammed Sani II, a gadon sarauta.
Allah Ya Karawa Sarki Lafiya Da Nisan Kwana ๐
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, Shugaban Majalissar Sarakunan jihar Jigawa ya isa Masarautar Keffi domin halartar bikin dabar cikar shekaru 10 ta Mai Martaba sarkin keffi, Dr. Shehu Chindo Yamusa.
12.12.2025