A Legas jiya, babban bankin ya bukaci bankunan da su bi umarnin da aka ba su na zuba sabbin takardun kudi a ATMs na bankunan su domin tabbatar da cewa sun fara yawo a ko ina.
CBN Ya Yi Barazanar Sanya Takunkumi Ga Bankunan Kasar Kan Kin Zuba Sabbin Kuɗin a ATM
Babban bankin Najeriya ya yi gargadin cewa zai hukunta bankunan da suka ki bin umarninsa na fitar da sababbin N200, N500 da N1,000 da aka sauya wa fasali daga Na'urorin Cirar Kuɗi na bankunansu
CBN ya yi wannan gargadin ne a jiya talata ta bakin Daraktan Sashen Ayyuka na Kudi na CBN, Ahmed Umar, a wani taron horas da daraktocin hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) na jihohi a Abuja.
Kotu ta dakatar da Gwamnatin Jihar Kano daga yunkurin da ta ke yi na gina shaguna a jikin Makarantar Sakandiren Kwakwachi.
Karin Bayani: https://t.co/MF9zgFz6Yk
Kamfanin haƙar ɗanyen man fetur na Shell zai biya diyyar dala miliyan 16 ga wasu manoma a yankin Neja-Delta da ke a kudancin Najeriya.
Karin Bayani: https://t.co/StQ1MIX4tV