Ba kowane murmushi ba ne ke ɗauke da gaskiya ba, haka kuma ba kowace yarda ba ce ke nuna amincewa ba. Wani lokacin, mutane suna fahimtar juna fiye da yadda suke nunawa, amma kowa ya zaɓi ya ci gaba da rawar da yake takawa.🎭
@OPay_NG Dear @OPay_NG , we want you to know that this program is just a scam. However, it seems we suspect that you might be in cahoots with them to defraud poor Nigerians. If we confirm this, expect our feedback.
Babban kuskuren da mutum yake yi shi ne ɗaukar lokaci a matsayin wani abu da yake da yawa. ba tare da ya fahimci cewa wasu damarmakin ba sa dawowa ba. Wata rana abin da yake kira shiri zai koma nadama, domin lokaci bai taɓa tsayawa jiran wanda bai shirya ba.
Babban abin takaici shi ne mutum ya shafe rayuwarsa yana jiran samun damar yin rayuwa, har sai ya fahimci cewa jiran da yake yi shi ne ya hana shi rayuwa.
Akwai wani irin ciwo da mutum yake ji idan ya waiwaya baya ya tuna da wanda ya kasance, amma ya kasa gane yadda ya zama wani daban. Abin da ya fi ciwo shi ne yau yana da fahimtar da za ta ceci tsohon kansa, amma ba zai iya komawa ya gyara abin da ya riga ya canza shi har abada ba
Neman abin da ba ka da shi na iya sa ka makance ga darajar abin da kake da shi. Ba kowace ni’ima ba ce ka yi burinta kafin ta zo maka ba, don haka kada burin gobe ya hana ka jin daɗin alherin yau.
Kwatanta rayuwarka da ta wasu na iya sa ka raina ci gaban da ka samu, domin kana ganin inda suka kai ne, ba ka san abin da suka fuskanta ba. Ba kowa ba ne yake da irin nauyin da kake ɗauke da shi ba, don haka jinkirin da kake gani a rayuwarka ba alamar gazawa ba ce.
We don’t need to think alike to understand each other. Listening to differing views teaches us because disagreement isn't always wrong. The real issue is taking dissent personally. Respecting differences matters far more than trying to prove you're right. 🧵👇
Sometimes, getting what you want is precisely what requires you to guard your heart, so that the blessing you have received does not make you forget the One who gave it to you.
@whitenigerian Who told you Nigeria is Lebanon? 😁😃 Ever since you were threatened with taking away your massive plot of land in Abuja, you returned to doing PR for Tinubu. 😁😀