Thinking of where to send your stablecoins, BNB and solana, convert to Naira and withdraw to your bank account instantly?
Try https://t.co/7LwAHVyi0U or download it on playstore.
No P2P wahala or stress, no liquidity issues what you sent is what you receive.
WATA BIYU KACAL DA FARA TAFIYA! SHIN KUN SAN ABIN DA NOVACHAIN ACADEMY TA CIMMA?
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!
Babu abin da zamu iya cewa ga Allah (SWT) bayan godiya a kan wannan babbar ni'ima da Ya yi mana ta samun gagarumar nasara cikin watanni biyu kacal da fara tafiyar NovaChain Academy, A cikin wannan ɗan ƙaramin lokaci, mun samu damar aiwatar da abubuwa da dama waɗanda suka ƙara tabbatar mana da cewa tafiyar da muka fara tana da muhimmanci kuma tana da tasiri a cikin al'umma.
GAYYATAR MASANA DA MASU KWAREWA
Daga cikin abubuwan da muka gabatar a cikin waɗannan watanni biyu, mun gayyaci masana da ƙwararru daban-daban domin su zo su raba iliminsu da ƙwarewarsu tare da community ɗinmu, musamman a fannonin Web3, Blockchain da sauran fasahohin zamani.
Daga cikin waɗanda muka gayyata akwai:
- Mahmud Galadanci
- Sanusi Danjuma Ali
- Aliyu Samba
- Barr. Abdullahi-Hadee Isah Ibrahim
- Aliyu Dahiru Aliyu
- Ahmad XM, wanda wani uzuri ya hana shi samun damar halartar shirin.
Muna matuƙar godiya ga dukkan waɗannan ƙwararru bisa lokacin da suka ba mu da kuma ilimin da suka zo suka raba tare da al'ummar NovaChain Academy. Hakika, al'umma ta amfana da gwala-gwalan ilimi daga gare su.
GOYON BAYAN AL'UMMAR CRYPTO
Haka kuma, mun samu gagarumin goyon baya daga ƴan Crypto, manya da ƙanana, waɗanda duk da cewa ba sa cikin shirin karatunmu kai tsaye, sun taimaka mana ta fannoni daban-daban bayan sun fahimci manufar da muke da ita da kuma irin sauyin da muke son samarwa a Arewacin Najeriya.
Daga cikin waɗanda suka ba mu goyon baya akwai:
Chizo1germany, Rabi'u Biyo, Engr. Bakaka, Imamu Sheka da sauran waɗanda suka taimaka mana ta hanyoyi daban-daban, Muna matuƙar godiya gare su, kuma muna addu'ar Allah Ya saka musu da alheri.
ƘARUWAR YARDA DA TASIRIN NOVACHAIN A CIKIN AL'UMMA
Alhamdulillah, muna ganin yadda mutane suke ƙara fahimtar manufar NovaChain Academy da kuma muhimmancin ilimin da muka zo da shi, Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara tabbatar mana da hakan shi ne yadda muka samu ɗimbin mutane suka yi registration domin fara karatunmu a ranar 1 ga Oktoba, 2026, duk da cewa tafiyar Academy ɗinmu ba ta wuce watanni biyu ba, wanda har yanzu ana ci gaba da samun sababbin masu registration.
Haka kuma, yadda social media platforms ɗinmu suka samu ɗimbin mabiya cikin wannan ɗan ƙaramin lokaci ya ƙara tabbatar mana da cewa saƙonmu yana isa ga al'umma, kuma akwai mutane masu sha'awar samun ingantaccen ilimi a fannonin da muka mayar da hankali a kansu.
COMMUNITY ƊINMU A SOCIAL MEDIA
1. Facebook: muna da Mabiya 10,990 Link: https://t.co/M5UHq05xu2
2. Telegram Channel: Muna da Mabiya 4,292 Link: https://t.co/qh6v80pqfO
3. WhatsApp Channel: Muna da Mabiya 2,478 Link: https://t.co/61KgV73ETz
4. X (Twitter): Muna da Mabiya 1,364 Link: https://t.co/ci4Sz3F5k3
MENENE MAKOMAR NOVACHAIN A SHEKARU BIYU MASU ZUWA?
Idan Allah Ya nuna mana wannan irin nasara cikin watanni biyu kacal, to muna kallon shekaru biyu masu zuwa da kyakkyawan fata da kuma babban buri, Insha Allah akwai gagarumar tafiya a gabanmu, Ba mu san irin girman abin da Allah zai kai mu gare shi ba, amma muna da yakinin cewa idan muka ci gaba da aiki da gaskiya, jajircewa, ilimi da kyakkyawar niyya, za mu iya ganin abubuwa masu girma a nan gaba.
Babban burinmu shi ne Allah Ya karɓi niyyarmu, Ya taimake mu wajan cimma manufarmu, Ya sanya wannan tafiya ta zama sanadin amfani ga al'umma, musamman wajan bunƙasa ilimi da ƙwarewar matasa a fannonin fasahohin zamani, Fatanmu shine kada Allah Ya bar mu da ƙarfin kanmu. Ya duba niyyarmu da manufar da muke da ita ga al'ummarmu, Ya ba mu hikima, ƙarfin guiwa da ikon sauke amanar da muka ɗauka.
Muna ƙara mika godiyarmu ga Allah (SWT), sannan muna miƙa saƙon godiya ga dukkan ɗalibai, mabiya, malamai, masana, masu ba da shawara, masu goyon baya da duk wanda ya kasance wani ɓangare na wannan tafiya, Muna kuma neman ƙarin Addu'a daga gare ku.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu.
NOVACHAIN ACADEMY
22/09/2026
This Samsung Galaxy S24 Ultra could be yours!
Just follow these simple steps to stand a chance to win it:
• Follow @gramvoicehq
• Follow @jacob_gramvoice
• Retweet this post
Do these three easy things today for your chance to win the Samsung Galaxy S24 Ultra!