Mun tashi mun samu iyayenmu Mata suna zaune cikin rufin asiri basu zuwa ko ina sai inda ya kama dole, kuma basu korafi, don ana biya musu bukatu daidai gwargwado, kowannensu yasan ibada yakeyi, amma yau da yawan matasa maza da mata basu dauki aure a matsayin ibada ba...โ๐ผ
"Dukkanmu daga Adamu muke kuma Adam daga kasa yake, babu fifikon balarabe akan baki, ko baki akan balarabe sai da tsoron Allah"
#Hadith
Don haka kabar wani feleke kana tinkaho ko kana girman Kai don kai fari/baki, mai kudi ko mai mulki ne, bakafi kowaba..
Tunatarwa Ce๐
Allah Sarki Dan Adam.๐
Duniya mai kyale kyale da yaudara, Tsohuwace tayi zamani da kakanka, tayi da babanka yanzu tazo tanayi dakai.
Kasani yadda taga bayan wadancan haka kaima zataga bayanka za'a wayi gari babu kai babu Ni.
Kabi Allah kadai shine tsira.
Tunatarwa Ce๐
"If you want to find out who your true friends and family are; become unemployed, get sick, or go through tough times. That's when you see everything clearly."
Sau da yawa wasu mutane na tunanin suna da wayau, idan suka yi haka, suka yi haka za su samu abin da suke so, akwai abubuwa da yawa da ba wayan mutum ba ne