A Microbiologist,A Biologist,An advocate of Public Hlth Educn. & Promotion.I like news,sports,science & politics.Tweets are purely my opinions #TeamData#TeamOR
🚨BIG NEWS!!!!
Alejandro Balde will join Manchester United, with both clubs now negotiating on the transfer fee. 🇪🇸🔴 #MUFC
FC Barcelona; already given the green light for Balde to travel to MUFC For medical if they agree a fee.
Personal terms are 100% agree with 5-year contract set until June 2031 with an option.
Hansi Flick have made it clear to Balde and Jorde Mendez, the player is not in his plan.
Busy week ahead! More to follow soon! 👀⏳
Congratulations to DSS Detective Assistants and Detective Inspectors as you are starting your journey, some of you will see this tweet after six months 🤝😎
How to Become a United Nations Online Volunteer
The United Nations Volunteering (UNV) programme offers a simple way for individuals to contribute their skills to global development initiatives—entirely online and from anywhere in the world.
Who can join?
Age: 18 years and above
Education: No special degree required
Mode: Fully online (work from anywhere)
Cost: Free and open to everyone
How it works
- Create an online volunteer profile
- Browse available volunteer assignments
- Apply to tasks that match your skills and interests
- Support UN agencies, NGOs, and development projects remotely
More details:
https://t.co/x4RFocoNoP
Direct application: https://t.co/hwGAy00wxa
Credit: United Nations Volunteering (UNV)
This update is shared by the Professor Isa Pantami Foundation as part of its commitment to promoting education, empowerment, and community development across Africa.
This opportunity aligns with the Foundation’s mission to promote education and academic excellence.
#PIPFoundation #ScholarshipOpportunities #UNVolunteering #OnlineVolunteering #GlobalOpportunities #EducationForAll
Tsakanin Dangote da PENGASSAN
Irin tankiyar da ake tsakanin Dangote da PENGASSAN za a rika samun ta a wannan lokacin da manyan abubuwa suke kaura daga hannun gwamnati zuwa hannun yankasuwa.
A aikin gwamnati akwai kariya da ma’aikaci ke samu na cigaban aikinsu muddin ba laifi ya aikata ba ko matsala ta shafi ma’aikatarsa ba. Illan wannan a Najeriya shi ne ya haifar da wofantar da aiki da ma’aikata da yawa suke yi kuma ofishin Shugaban Ma’aikata da kungiyoyin kwadago suna hana ladabtar da su kamar yadda doka ta tanada.
Wannan rashin ladabtarwa shi ne babban dalilin lalacewar aikin gwamnati da hukumominta da kamfunnanta wadanda aka kafa don amfanin jama’a.
Da aka lalata na gwanati sai aka samu gibi da yankasuwa suka shigo suka kafa nasu kamfunna akasari da kudaden jari da ya hada da na yankasashen waje. A nan, dole abin ya taho da matsaloli biyu amma idan aka sa hankali a lamarin za a iya warware su.
Matsalar Ma’aikaci
Na farko dole ma’aikata su sani cewa ba za su samu kariya irin wacce suke da ita a gwamnati ba. Kasuwanci ba ya aiki da haka. Dole su tashi tsaye su yi ta aiki wurjanjan ko da a albashi da bai kai na gwamnati ba a sau da yawa. In kuwa ba su yi, su ajiye aikin su tafi su nemi wani wajen kamar yadda da yawa suka yi hatta a matatar Dangoten.
Haka ita ma Gwamnati da kungiyoyin kwadago ba za su iya bai wa ma’aikaci kariya a kamfanin dankasuwa ba a ko wane hali kamar yanda suka saba yi a na gwamnati. Amma suna iya shiga tsakani a kan abinda bai shafi laifi ba ko hakkin dankasuwa ba wanda doka ta ba shi.
Matsalar Dankasuwa
Matsala ta biyu ita ce ta dankasuwa. Burinsa riba ne, ba kyautata wa al’umma ba. Haka Adam Smith ya ce. A wajen neman riba, in aka bar shi, zai iya aikata komi, kuma ya take kowa. A nan dole a taka masa birki.
Masu taka masa birki Allah ne da dokokin kasa. Dole ya ji tsoron Allah musamman in ya yi imanin haduwa da shi kar ya ci zalin ma’aikatansa, amma ya ba su hakkinsu bisa adalci har ma ya kyautata musu saboda Allah na son masu kyautatawa. In ya ki, ya yi gaban kansa, to Allah na madakata yana jiran sa.
Dole kuma gwamnati da kotuna su tabbatar sun samar da dokoki da za su hana cin zalin ma’aikata da musguna musu. Wadannan dokoki idan akwai su dole a tashi tsaye wajen dabbaka su. Hakkin yankasa ne da ya zama wajibi a kan bangarorin gwamnati guda uku duka. Inda dokokin suka gaza, sai majalisa ta kyautata su amma ba tare da sun daure hannun yankasuwa ba ta yadda za a koma gidan jiya inda ma’aikata da kungiyoyinsu za su lalata kasuwancin kamar yanda suka lalata na gwamnati a baya.
Kira
Babban kirana a nan shi ne sassan biyu su wa Allah su sasanta tsakaninsu. Kai Dangote ka yi abinda Allah ya ce. Ka duba korafin ma’aikatanka yan Najeriya ka ba su daraja kamar yanda kake bai wa Indiyawan da ka kawo. An sani akwai kudaden da za ka kashe wa yanwaje (expatriates) wandanda a ka’ida ba sai ka kashe wa yan Najeriya ba saboda bambamcin rayuwa tsakanin kasashensu da nan. Ma’aikatu na waje da yawa haka suke yi. Amma, a kalla, basic salary dinsu ya kasance daya ko kar tazarar ta yi yawa. Ko ka biya su kusan abinda sauran yankasuwa—kamar BUA, Shell, Otedola da sauransu—suke biyan ma’aikatansu. Kar giyar kakagida (monopoly) ta kwashe ka ka ce abinda ka ga dama za ka yi don ba yanda Najeriya ta iya da kai a harkar mai a yanzu, kai ne kadai damisa a fage. La! La!
Ku kuma PENGASSAN dole ku sani zamani ya wuce da za ku ci karenku ba babbaka a Najeriya. Idan kuna tuhumar Dangote da karya dokar kwadago, ba rufe matatarsa da tirsasa shi da karfi zai gyara abun ba. Kotu ke da hakkin tirsasa shi idan ta tabbatar da laifinsa. Don haka sai ku maka shi a kotu. To a nan ne za a warware matsalar lokaci guda har a ba da hukunci da zai yi amfani nan gaba idan yanayi irin wannan ya taso. In ba haka ba, mu yan Najeriya ku za mu dora wa laifi.
Fata
Ina fata Allah ya sa biyun su daidaita tsakaninsu. Mu dai fatarmu bunkasa tattalin arziki, da fahimtar juna da bin doka.
Allah ya taimake mu.
Dr. Aliyu U. Tilde
29.09.25