Mafi tsadar lokacinda Allah yake Bayyana Mu’uminai tsantsa da Munafukai tsantsa yazo!
"من فرح بنا فرحنا به"
Muna taya Mu’uminai Farinciki da Watanda Allah ya haskaka Dunia yayinda take tsananin duhu!
أهلا بشهر المصطفي ﷺ
Salati Da Gaisuwa Ga Mafificin Halitta ﷺ
سَلَامٌ عَلَى خَيْرِ الْبَرِيَّةِ مَنْ بَسَطْ
مَوَائِدَ دِينِ اللّٰهِ فِي شَكْلِهِ الْوَسَطْ
Fassara:
Aminci da salama su tabbata ga mafificin halitta ﷺ,
wanda ya shimfiɗa koyarwar addinin Allah cikin hanya madaidaiciya da matsakaiciya.
💭 Manzon Allah ﷺ shi ne rahama ga talikai, kuma ta hanyarsa Allah Ya cika ni'imar addini. Ya koyar da al'ummarsa tafarkin adalci, tausayi, hikima, da daidaito. Don haka wajibi ne mu ƙaunace shi, mu yawaita yi masa salati, mu kuma yi koyi da Sunnarsa a cikin rayuwarmu.
🤲 اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا محمد، وعلى آله وصحبه أجمعين.
Ya Allah! Ka cika zukatanmu da ƙaunar Manzon Allah ﷺ, Ka ba mu ikon bin Sunnarsa, Ka kuma tara mu tare da shi a Aljannatul Firdausi.
In ban da rashin kunya ta yaran zamani masu da'awar malunta, yanzu kai ko duniya ka shigo ka ga abu da irin su Sheikh Sharif Ibrahim Sale (R) a ciki, ka tsaya tambayar hujja: ina wannan abu ya samo asali.
Sharif Sale fa, saboda girman da Allah ya yi masa a cikin wannan addini, jahilai ma ba sa iya magana a kansa. Shi, idan ka ji mutum yana magana a kansa, to mai maganar ba wawaya ba ne; domin jahili ba ya bayyana malami. Sharif, daga ƙasashen da ake ɗaukar nauyin Wahabiyawa ake zuwa wajensa ɗaukar karatu. Shi, ilimin da Allah ya ba shi ya fi ƙarfin iya mutanen Najeriya su kwashe shi; duniya ce gaba ɗaya za take zuwa ɗaukar iliminsa.
Amma duk da haka, shi muridin muridin muridin Shehu Tijjani ne (R). Shi ya sa idan na ɗaga kaina na kalli Sharif, sai na yi wa Allah godiya, kasancewar ni da shi mun yi tarayya a da'ira ɗaya ta ɗarika.