Kwalejin koyar da aikin jinya da kimiyya ta jihar Kebbi, tayi martani ga kalaman da fitacciyar 'yar TikTok kuma tsohuwar dalibar makarantar Rahama Sa'idu tayi, biyo bayan korarta da ta ce kwalejin tayi.
Sanarwar da kwalejin ta wallafa a shafinta na sada Facebook. #arewacele
Hukumar tsaron DSS a Najeriya ta saki tsohon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC Abdulrasheed Bawa.
Bawa ya kwashe tsawon watanni tsare a hannun hukumar ta DSS, wadda ta ce tana tuhumar shi da aikata wasu laifuka.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sake tura Engr. Abubakar Momoh daga Ma’aikatar Matasa ta kasar zuwa ma’aikatar raya yankin Neja-Delta.
Wasu daga cikin ministocin sun hadar da Adegboyega Oyetola a matsayin ministan ruwa da tattalin arziki.
Kylian Mbappe, mai shekara 24 a duniya, ya ce zai cigaba da zama a PSG har zuwa karshen shekarar 2023, sai dai fa a shekarar 2024 Real Madrid kadai zai takawa leda. #PSG#RealMadrid#Mbappe
Shugaba Najeriya Bola Tinubu ya fara duba yiwuwar dawo da tallafin man fetur na wucin gadi, adaidai lokacin da farashin danyen mai da kuma farashin musayar kudaden waje ke cigaba da hauhawa a kasar.
Sai dai rahotanni sunce har yanzu ba’a yanke hukunci na karshe akan batun ba.
Dan takarar shugabancin Najeriya na Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya kai ziyara ta Musamman ga Takwaransa Injiniya Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso a gidansa dake Abuja a daren nan.
Sanata Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa “ina godiya da wannan ziyara”.
Shugaban kungiyar dillalan man fetur din na Najeriya Chinedu Okoronkwo ya ce matuƙar dala zata tashi ba shakka farashin man fetur shima zai tashi.
Acewarsa, basa iya samun dala a bankunan kasuwanci kuma idan kaje kasuwar bayan fage farashin ya wuce tunani. #DNNHausa
Sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar sun sha alwashin hallaka hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum idan har makwabtan kasashe suka yi yunkurin daukar matakin soja a kansu.
Sojojin sun ce wannan ne martanin da suma zasu mayar batare da bata lokaci ba. #DNNHausa
Yanzu haka dai jagoran tawagar kungiyar kwallan kafa ta Najeriya Ahmed Musa ya baiwa Karkuzu kyautar naira dubu dari biyar, tare da umarnin a nemo gida da bai haura miliyan biyar ba ya Siya masa.
Wannan na nufin ��ungiyoyin Kannywood basu da asusun tallafawa yan:uwansu kenan?
Dije Abdu Aboki ita ce mace ta farko a tarihin jihar Kano dake Arewacin Najeriya da ta zama Cif Joji, wato alkaliyar alkali.
Wane irin cigaba kuke fatan zata kawo wa bangaren shari'a a jihar Kano?
Shugaban mulkin soji na jamhuriyar Niger, Janar Abdourahmane Tchiani ya sanar da sunan tsohon ministan kuɗin ��asar a matsayin sabon firaminista.
Ali Mahaman Lamine Zeine ya maye gurbin Mahamadou Ouhoumoudou wanda yake Turai lokacin da aka yi juyin mulkin.
Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance tare da tabbatar da sunan mutane 45 daga cikin 48.
Ministocin da majalisar bata tabbatar da nadinsu ba sune:
Nasir El-Rufai - Jahar Kaduna
Sani Abubakar Danladi - Jahar Taraba
Stella Okotete - Jahar Delta
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ce babban abin da ya fi da cewa da Najeriya a wannan zamani shi ne mulkin dimokradiyya.
Ya bayyana haka a bikin yaye manyan sojoji wanda makarantar yaye manyan hafsoshi ta Jaji da ke jihar Kaduna tayi.