Tunda kai ba zaka yi masa hanya ya sameta ba, meyasa ba zaka rufe bakinka ka wuce ba?
Kai Basimpe!
F00l. Stop!
Don Allah idan an samu wannan shafal-shafal a kira lambar nan a hadata da Innocent Man kai lambar.
Akwai takaici kaga namiji yana comment a karkashin irin wannan post yana kokarin sukar wannan bawan Allah da yake neman mata shafal-shafal.
Bai ce dole sai ka bashi 'yarka ko kanwarka ba. Hasalima basu da wadannan qualities din. To ina ruwanka dashi?
....
A matsayinka na Innocent Man, dole ka san cewa kowace mace tana da wani namiji da baya laifi a wajenta. Koda bai bata ko sisi ba, yafi wanda ya bada dubu malala. In ba kai bane. To ba kai bane. Kar ka kashe kanka. Fool. Stop!
Menene Alphanci?
Thread!
Abu na farko da zaka fahimta shine Alphanci ba wai zance ne akan mata ba. Alphanci karatu ne na inganta rayuwarka a matsayinka na Innocent Man. Zancen mata yana shigowa ne kadai saboda wasu shashashai da ake ce musu Simpopi.
Abu na biyu mai matukar muhimmanci a Alphanci shine Manufa. Wato "Purpose". Ba a yin Alphanci babu manufa. Dole kana da wani gagarumin abu da kake cikin aikin cimmawa, dare da rana. Dole ka zama kana da Purpose. Purpose dinka yana da alaka da Values dinka.