Yan Bidi’a sun yanke Karatun Shiekh Aminu Daurawa akan Auren Mutu’a kamar yadda suka saba sharri.
Saurara Raddin Shiekh Daurawa akan Mas’alar, Malam ya tabbatar da Auren Mutu’a Haramun ne…!!
Rarara is not a man of integrity, he doesnt deserve any attention from Professor Pantami, I’d be sad if Sheikh even responds to a betrayer and snake like him.
Have we all forgotten how irrelevant Rarara was, and President Muhammadu.m Buhari made him rich and famous? First thing he did as PMB’s tenure ended is hold a very irrelevant conference call to call out Buhari.
Why is he even getting any attention right now please? If disrespecting people whom Allah has highly blessed is his means of getting food, allow him please.
Idan ka auri mace, amma da niyyar kawai ka ji daɗi zuwa wani lokaci sai ka sake ta, sunan shi Ha'inci; Ka cuce ta, ka ɓata mata lokaci domin ita ta aure ka ne domin a yi zaman har abada. Idan kuma ka sa lokaci, sunan shi Mut'ah kuma Annabi ya Haramta.
Malam ya ce, ka ɗauki matar ka tafi da ita.
Mata su ma mutane ne, kuma Allãh Ya basu ƙima da daraja a addini.
Shugabanci nagari yana samuwane kawai daga mutane nagari. Mun dade muna kushe mutane nagari muna koresu tare da tsoratasu daga shiga harkokin siyasa muna cewa wai ai siyasa ta mutane ashararu ce. Kuma a haka muke sa ran ashararu suyi abunda ya kamata.
Indai har kana son shugabanci nagari kuma kake tsangwamar irinsu Malam Isah Ali Pantami kan sun shiga siyasa to kodai karya kake ko kuma baka san inda ke maka ciwo ba.
Daga lokacin da ka yadda mutanen banza ne kawai ya kamata su shiga siyasa to bakada huruma tsammatar abun kirki daga mutanen banza.
Ko da a yanayin siyasa, akwai mutanen da darajarsu ta wuce a rika ci musu mutunci saboda irin gagarumar gudunmawar da suka bayarwa ga al’umma. Sheikh Pantami yana daya daga cikin su a mahanga ta. Bai kamata masu yi masa adawa su fi mayar da hankali wajen cin mutuncinsa, maimakon su yi masa adawar ta hanyar hujjoji, ra’ayi da bambancin siyasa ba.
Ba mamaki samun nasarar Professor Pantami ya canja akalar siyasar Arewa.
Idan Malam ya samu nasara, ya buga misali na kyawawan shugabanci a Gombe, tabbas zai ƙarfafawa mutane da yawa gwiwa a sauran Jihohi suma su shiga a dama da su a shekaru masu zuwa.
Wataƙila anan Kano sai kaji irin su Dr. Bashir Aliyu Umar, ko Prof. Sarki Abba suma sun shiga domin kawo gyara da samar da nagartaccen shugabanci.
Allah ya taimake mu, Ameen.
Insha Allah wannan haukan da Rarara yayi saboda ya burge wani dan siyasa shine dalilin faduwar dan siyasar.
In Allah ya yarda sai Malam Pantami yayi nasara a Gombe.