Ba ta da wani abu na musamman...
Kawai dai bakayi soyayya da mata da yawa bane.
Kulla alaka da mata da yawa za ka ga tsarin halayensu yana maimaita kansa da kansa.
Irin barkwancinsu daya.
Irin yaudararsu daya.
Irin saukin su daya.
Irin cewa ni ba kamar sauran ‘yan mata bane daya.
Komai yana maimaita kansa.
Kana cewa ita daban ce ne saboda...
Tana mayar maka da sako
Tana nuna yar karamar sha'awa akanka
Tana ba ka yar kauna kadan
Wannan ba wani abin kallo a fada ba ne.
Wannan shi ne mafi karanci.
Maza ba sa shakuwa da mata.
Suna shakuwa ne da yadda mace ta sa suka ji lokacin da suke jin yunwar samun kulawa.
Idan zabin da kake da shi kadan ne, kowace 'yarinya mai kyau tana zama kamar wata mu'ujiza a gare ka.
Wannan ba soyayya ba ce.
Wannan karancin abubuwan dogaro ne (scarcity).
Ba ita ce macen da kake tunsnin an halitta domin rayuwarka ba (soulmate).
Kawai dai ita ce zabinka na yanzu da ka fi so a cikin jerin sunayen mata.
Babban bambanci ke nan.
Kuma da zarar ka ga wadannan abubuwan suna maimaituwa sosai, za ka daina dora ta a matsayin abin bata kai ba.
Za ka fara kimanta ta da hankali.
Ba kaine Ka canja ba idonka ne kawai ya bude yanzu.