Dan uwa/Yar uwa..
Dauko Alqur'aninku, ko izu 1 ka karanta akwai dimbin lada, ko wani harafi daya lada 10.
Kanaga lada nawa zaka samu in ka karanta haruffa dubu 3?
Watarana Manzon Allah SAW yana kan mimbarinsa yana Khudba, sai ya hango Jikokinsa (Hassan da Hussain) sun fito gida suna sauri zasuzo wajensa suna faduwa a kasa, sai SAW yayi sauri ya sauko daga mimbari yaje ya kamosu ya shigo dasu masallaci ya daurasu kan mimbari sai yace: Hakika Allah yayi gaskiya, Allah Yace: "Lallai Dukiyoyinku da Yayanku fitina ce a gareku" ka dubi tsantseni/sanin girman Allah na Manzon Allah amma yana khudba baisan lokacin da ya yanke ya fita ba saboda Jikokinsa..💔
Note: Hakika Yayanmu jarabawa ce garemu, karmu bari soyayya ta hanamu yi musu Tarbiyyar addini..
Allah yasa mu dace..🤲🏼
Manzon Allah SAW yace:
"Ka zama cikin mutane 4 amma karka zama na 5 sai ka halaka.
Ka zama:
1️⃣Malami
2️⃣Dalibi
3️⃣Mai sauraro
4️⃣Mai tambaya
Karka zama na 5 sai ka halaka.
Na 5️⃣ shine Jahili, baya tambaya, baya sauraron karatu, baya zuwa daukan karatu kuma shi ba malami bane.
A yanzu kayan da matan aure da yan mata suke sakawa suna zuwa gym namiji ma mai mutunci bazai iya sakawa ba balle mace,
Haba ina kunyarki?
Ina addini?
Ina tarbiyya?
Shi kenan ku duk abunda arna sukeyi sai ku kamayi wai shine wayewa.
Wannan halaka ne da tabewa..✍️
Wajibi ne ga kowani Musulmi Namiji da Mace Yasan wadannan abubuwa:
1⃣Farilla(Wajib)
2⃣Halal
3⃣Sunnah
4⃣Haram
5⃣Makruhi
6⃣Mustahabbi
7⃣Mubahi
8⃣Mandubi
9⃣Shubha
Don kasa komai a matsayinsa, karka gauraya Halal da Sunna, ko Makruhi da Shubha..
Allah yasa mu dace..🤲
Shi neman Ilimin #Addini Wajibi ne ga kowani Musulmi namiji/Mace, Ba Zabi bane Dole ne, bakada Uzuru a Lahira wai kace baka nema ba.
Amma ka nemi na boko don ana samun Kudi dashi a duniya..
Duk wanda yayi kuskuren zuwa lahira da Jahilci zai yabawa Aya Zaqi
Inkunne yaji..👂
Ku Guji aikata laifuka 7 Masu Halakarwa:
1⃣Shirka
2⃣Tsafi (Sihiri)
3⃣Kashe Rai wacce Allah ya Hana sai dai da Hakki
4⃣Cin Riba
5⃣Cin Dukiyar Maraya
6⃣Guduwa a fagen Yaqi
7⃣Yin Kazafi wa Mata Katangaggu muminai
#Hadith