🎯 NEXT VIDEO: YADDA AKE ON-CHAIN ANALYSIS!
A yau za mu koyi yadda ake amfani da Exchange Inflow da Outflow wajen fahimtar motsin kuɗin crypto a kasuwa.
Akwai abubuwa biyu da ya kamata ka riƙa dubawa:
1️⃣ Exchange Inflow (Shigar Coins Exchange)
Wannan yana nufin lokacin da ake tura coins daga wallets zuwa Crypto Exchanges.
Idan ka ga coins suna shiga exchange, yana iya zama alamar cewa masu riƙe da su suna shirin sayarwa. 📉
2️⃣ Exchange Outflow (Fitar Coins daga Exchange)
Wannan kuma shi ne lokacin da ake cire coins daga exchange zuwa private wallets.
Idan ka ga coins suna fita daga exchange, yana iya nuna cewa masu riƙe da su suna son ajiyewa na dogon lokaci (Holding).
A wani lokacin kuma, yana iya kasancewa ana shirin yin OTC trading.
3️⃣ Menene OTC Trading?
OTC na nufin Over-The-Counter.
Wato ciniki kai tsaye tsakanin masu saye da masu sayarwa, ba tare da yin cinikin ta hanyar order book na exchange ba.
🔥 Me ya sa wannan yake da muhimmanci?
Domin ba sai ka jira chart ya nuna maka komai ba. On-chain data na iya taimaka maka fahimtar abin da ke faruwa da coins kafin ka yanke shawarar shiga kasuwa.
Ka tuna: Inflow ba lallai yana nufin za a sayar ba, haka Outflow ba lallai yana nufin Holding ba.
Ka haɗa su da sauran market data kamar chart dinka da volume kafin ka yanke hukunci.
Learn to read the blockchain. Don't just follow the crowd!
#CryptoEducation #OnChainAnalysis @BitkovaHub
Yau zamu tattauna akan three layers of the internet wato wasu matakai guda uku na Internet;
1. Surface Web.
2. Deep Web.
3. Dark Web.
Sau da yawa mutane suna tattaunawa akan Web1, Web2 da Web3, akwai bukatan fahimtar surface Web, Deep web da kuma dark web.
Idan ka kalli hoton dake kasan wannan rubutun zaka ga hoto kamar Kogi, a cikin sa akwai kankara irin mai girman nan wanda ya nitse har kasan ruwa, wato Iceberg da Turanci. Toh ka tsaya ka kalli hoton sosai sai ka dawo ka karanta wannan rubutun da kyau.
1. Da farko idan aka ce Surface web ana nufin wani waje a Internet wanda kowane mutum zai iya shiga ya duba duk abinda yake so ta hanyar yin amfani da search engines da kuma browsers.
A bangaren Surface web ana nufin wani yanki na internet wanda zaka iya shiga ka leka abubuwan da suke cikin Google, Yahoo, Bing, da sauran su ta hanyar taimakon browser dake kan wayar ka ko computer ka, kamar Chrome, Safari, Opera Mini, Fox da sauran su.
A karkashin Surface zaka iya shiga website kala daban daban ka duba abubuwan da kake so, zaka iya leka Public blogs da dama, zaka iya hawa Facebook, Twitter da sauran su. Wannan shine Surface web ko Indexed Web.
2. Deep web, ana nufin wani bangare na internet wanda ba zaka iya shiga ba sai ka samu izini, kamar email dinka ba zaka iya shiga ba sai da login details, kamar email din wani mutum ba zaka iya shiga kaga abinda ke ciki ba sai an baka logis credentials din.
Shi Deep web wani yanki ne na internet da ake jibge sirri da bayanai da sirrori kala daban daban, misali private database, medical records na wani Private hospital ko public hospital, duk akwai bayanan mutane da sirrin su amma ba zaka iya lekawa ciki ba sai an baka izini ko an bude maka.
A karkashin Deep web akwai Bankuna, physical banks ko Virtual (Online) Banks, ba zaka iya shiga Opay dina kaga Naira nawa nake dasu ba sai na baka password ko passkey. Ana iya shiga cikin Deep web da taimako browsers kamar Chrome, Safari, Opera da sauran su.
3. Dark Web....
Wani bangare na internet da ba zaka iya shiga ta hanyar amfani da browser ba irin su Chrome ko Mozilla ko Opera Mini ba. A karkashin Dark web ba zaka iya sanin kowa da sunan sa ba saboda decentralized ne kuma ana amfani da additional encryption methods sosai akan sa.
Dark web wani waje ne da ba zaka iya shigan sa kai tsaye ba sai kayi amfani da Tor Network, ko I2P ko Freenet. Sai dai duniya tafi sanin Tor Network game da duk abinda ya shafi Dark web. Abinda yasa ake kiran sa da Tor Network wannan Tor din ana nufin "The Onion Routines".
Shi Tor Network asalin sa anonymous communication proxy network ne. Ta yadda duk lokacin da muka yi wata tattaunawa ko muka aike da wani sako ta cikin Tor Network da zaran mun kammala no record will remain ko stay on the network, ya gogu ko ya tafi.
A cikin Dark web akwai kasuwanni, akwai kafofin sadarwa na social media, wadanda sun sha banban da wanda ka saba gani.
Idan ka fahimci Dark web kamar dai wata duniya ce ta daban mai zaman kanta ta daban, bayan duniyar mu ta zahiri akwai duniyar internet, online kenan a online din kuma akwai dark web, wainar da ake toyawa a wannan online din da aka fi sani ta sha banban da sani Wainar da ake toyawa acan duniyar Dark web.
Kamar dai kace duniyar Aljanu, da duniyar Mala'iku da kuma wannan duniyar da mutane suke rayuwa cikin ta, kowace duniya akwai ta, kuma ana rayuwa ana sabgogi cikin ta.
Wasu suna shiga Dark web ta hanyar amfani da Tor browser, wasu suna amfani da Tails da sauran browsers da suke iya shiga duniyar Dark web.
Dark web yana da layers sosai, kamar yadda Internet yake da layers. Sun saka masa suna ne da The Onion Routines wato TOR saboda layers dinsa kamar yadda kaga Albasa yana da Riga kala kala daban daban, hawa hawa, daga wannan sai wannan, daga wancan sai wancan toh haka Dark web yake.
Dark web waje ne mai hatsarin gaske. Ana amfani dashi ta hanyoyin masu kyau, haka kuma ana amfani dashi ta hanyoyin marasa kyau.
KA INGANTA ANALYSIS DINKA [SPOT ONLY]
A wannan video na yi amfani da 1W timeframe wajen fidda support and resistance.
(Zaka iya amfani da 1D timeframe kajen fidda support da resistance).
Daga nan na gangaro zuwa 1H/4H don neman entry.
Wannan video ba Financial advice ba ne.
Na yi shi ne don ilmantarwa.
Kuyi like da retweet don amfanar sabbin traders.
A halin yanzu muna da stocks guda 146 a kasuwar NGX.
40+ stocks HALAL ne a halin yanzu, suna wakiltar kusan kashi 46% na kuɗin kasuwar NGX.
Sannan akwai Sectors guda 11.
- Financial Services
- Consumer Goods
- Industrial Goods
- Oil & Gas
- Telecommunications
- Agriculture
- Healthcare
- Construction / Real Estate
- Services
- Natural Resources
- ICT
--------------------
A yanzu haka Sectors guda huɗu (4) suke jan kasuwa:
- Banks/Financial Services,
- Industrial goods,
- Telecoms,
- Oil & Gas.
✅ Manyan sectors zasu baka steady growth.
✅ Kananan zasu baka quick gains, idan ka dace.
--------------------
Diversification (raba-kafa)
A babin diversification kada ka tara stocks sama da biyu wanda suke karkashin sector ɗaya.
- Saboda kana tara risk, idan aka sami changin a kudurin gwamnati, zai yi affecting ɗin portfolio ɗinka sosai.
- Idan sector ya ja baya, duk stocks ɗinka zasu grigiza.
- Ana iya samun cinkoso a sector ɗaya, sai nasararsu ya dakushe.
---------------------
Misali: BUA FOOD da DANGOTE SUGAR da CADBURY da NESTLE da NASCON (Consumer goods)
Ko MTN da AIRTEL (Telecoms)
Ko SEPLAT da ARADEL da CONOIL da ETERNA (Oil & Gas)
Ko LAFARGE da WAPCO da BUACEMENT da DANGOTECEM da JULIUS BERGER (Industrial goods)
JAIZBANK karkashin Banks
Ko FIDSON da May & Baker (Health)
--------------------
A wannan kasuwa, ba wanda ya fi kowa ilimi ke cin riba…Wanda ya fi kowa tsari da discipline ne ke cin riba.
Me kake jira, ka fara gina portfolio ɗinka na STOCK a yau.
Wace matsala kake fuskanta a tafiyarka ta investment a halin yanzu?
Credit: Sir @Mahmoudsardauna
Lead & CEO, Bitkova Academy