Duk lokacin da na ji muryar Malam Albany, sai in ji kamar an yi min allura ta ƙarfafa gwiwa. Domin Malam kullum yana cikin zaburar da matasa da ƙarfafa musu gwiwa wajen neman ilimi.
Hakika, malamai suna barin duniya, amma tasirin iliminsu da nasihohin su yana ci gaba da rayuwa a zukatan mutane.
Allah Ya jiƙan Malam Albany, Ya gafarta masa, Ya haskaka kabarinsa, Ya kyautata makwancin sa, kuma Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomar sa.