"...tun daga kan Badaru har Gerawan, ba zan sake bin umarnin kowa ba..." - in ji Yakubu Giredi Garki
Cikekkekiyar hirar tana nan zuwa da misalin karfe 9:00 na daren yau Talata a Sawaba FM 104.9 Hadejia.
An yi wata arangama tsakanin matasa da wasu da ake zargi da yunkurin yanka wani dajin makiyaya a karamar hukumar Kaugama ta jihar Jigawa
Al’ummar yankin Ubba a mazabar Askandu sun bayyana fargabar cewa yankan dajin na Aguyaka, wanda ya kai girman hekta 84 na iya haifar da rikici
#Gujungu: Akwai buƙatar kawo agajin gaggawa a garin Gujungu, Taura, jihar Jigawa bayan wata tankar mai ta kama da wuta.
Rahotanni daga mazauna garin na cewa, motar kwana-kwana da ta zo kawo agaji, ita ma da turi aka ƙarasa da ita. Ana fargabar wutar ta fara kama gidajen mutane
Shugaba Tinubu ya karfafa gwuiwa duk 'yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje da su komo gida. A cewarsa, tattalin arzikin Najeriya ya farfado tun bayan zuwansa kan mulki.
Mene ne ra'ayinku kan kalaman Shugaba Tinubu da jan hankalin da yake ga masu zama a kasashen ketare?
Ko kun gamsu da aiyukan da gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi suka aiwatar muku a cikin watananni 6 na wannan shekarar (2025), la’akari da kuɗin da gwamnatin tarayya ta raba musu don al’umma?
Mai magana da yawun jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ta bayyana cewa jam'iyyar za ta gudanar da taron Kwamatin Zartarwa na Ƙasa (NEC) a ranar 28 ga Agusta, 2025 a Abuja domin duba yiwuwar marawa Tinubu baya ko shiga kawancen jam'iyyun adawa a taron ta na koli.
Gaskiya lamari game da akwatin da Minista Badaru ya dangwala ƙuri'a a garin Ɓaɓura a zaɓen cike gurbi na ɗan majalissar tarayya mai wakiltar Ɓaɓura/Garki.