ALLAHU AKBAR!🙏🙏👇
Young and talented Gwani Musa Salihu Auwal has memorized the entire Qur’an and written it completely by hand.
A remarkable achievement that reflects a deep connection with the words of Allah. May Allah bless him and make the Qur’an a light and guidance in his life.
The Nigeria Police Force claims that the reported video was misleading. That the heavily armed men on bikes were members of a Vigilante Group and registered hunters. Pls @PoliceNG explain to us:
1. How a vigilante group is allowed to wear an army uniform.
2. Why a vigilante group is carrying heavy machine gvns.
3. Why some are masked up and don't have recognized uniforms like all vigilante groups in Nigeria.
4. Why the people in the video are loud and constituting a nuisance on roads.
Now since you claim these people are hunters, why are they allowed to posses machine guns that isn't authorized for civilians?
Once again, explain to the public why a vigilante or hunter is on army camouflage.
He was the first person in his family to accept Islam, and now 45 members of his family have also accepted Islam.
Insha'Allah, the message of Islam will reach every family.
Labari | Shaikh Sudais Ya Dawo Bayan Watanni Biyu!
A gobe babban limami a Haramin Makkah Shaikh Abdurrahman Sudai zai jagoranci sallar Magariba bayan shafe kusan watanni biyu ba tare da an ji muryarsa ba.
Ahlul Qur'an
@bmjvermerlleey Na 1: An yanke masa hukuncin kisa saboda ya yi zina tare da wata da ya haramta masa har abada (misali mahaifiyarsa ko 'yarsa) a wasu mazhabobi.
Na 2: An yanke masa hukuncin jefewa saboda muhsani ne (wato ya taba yin aure kuma ya sadu da matarsa).
✨🕌🌹 ZIYARAR BAN KWANA A FEZ, MOROCCO 🌹🕌✨
Alhamdulillāh, Maulana Sheikh Imam Junaidu Abubakar Bauchi (Hafizahullāh) ya kammala ziyarar ban kwana a Fez, Morocco, inda ya samu damar ziyartar Rawdat Maulanmu Shehu Ahmad Tijjani (RTA) da Zāwiyatu Tijjaniyya—gidan haske, gidan zikiri, da makoma ta soyayya ga salihai.
A wannan lokaci mai cike da shauƙi, hawaye na zuciya da nutsuwar ruhi, an yi ban kwana da jiki, amma ba ban kwana da soyayya ba. Zuciya tana nan a ɗaure da wannan wuri mai albarka, tana mai juyawa cikin shauƙin ƙaunar Allah da masoyanSa.
🤲 Ya Allah, Ka sanya wannan ziyara ta zama haske a rayuwa, Ka cika ta da ilimi mai amfani, Ka kuma haɗa mu da salihai a duniya da Lahira cikin rahamarKa.
✨ Ban kwana ne da idanu… amma ba ban kwana da ruhi ba.
🌹 Ban kwana ne da tafiya… amma soyayya tana nan har abada.
🇳🇬 WANNAN ITA CE NI'IMAR DA ALLAH YA YI WA NAJERIYA.
Sheikh Prof. Mansur Isa Yelwa (Hafizahullah)
ya tuna mana da wata ni'ima mai girma da Allah Ya yi wa Najeriya.
Ya ce:
Duk duniya, Najeriya tana daga cikin ƙasashen
da Allah Ya albarkata da yawan mahaddatan Alƙur'ani.
Har ma ya kawo maganar
Sheikh Ibrahim Al-Akhdar Al-Qayyim,
ɗaya daga cikin manyan malaman Alƙur'ani a Masallacin Annabi ﷺ,
Wanda ya bayyana cewa:
Mun yi ittifaqi cewa idan aka zo batun
Karatun Alƙur'ani gadan-gadan,
Najeriya tana daga cikin ƙasashen da suka fi ƙwarewa a duniya.
Wannan ba maganar alfahari kawai ba ce.
Wannan amanar Allah ce.
Amanar da ke nuna cewa Allah Ya ba mu wata baiwa
Da ya kamata mu kiyaye.
A kusan kowace gasa ta Alƙur'ani da Najeriya take shiga,
Ana ganin alamun wannan baiwa.
Ana ganin ƙoƙari.
Ana ganin jajircewa.
Ana ganin irin soyayyar da mutane suke yi wa Alƙur'ani.
Amma Malam ya nuna mana cewa:
Ba nasara kaɗai ake nema ba.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu taimaki addinin Allah.
Mu yi aiki da Alƙur'ani.
Mu koyar da shi.
Mu rayu da shi.
Mu ɗaukaka shi a rayuwarmu.
Idan Allah Ya ba ka Alƙur'ani,
To Ya ba ka wata ni'ima mai girma.
Kuma mafi kyawun godiya ga wannan ni'ima
ita ce ka kasance cikin masu hidima ga Alƙur'ani da addinin Allah.
🤲 Ya Allah, Ka ƙara wa Najeriya albarkar Alƙur'ani.
🤲 Ya Allah, Ka sanya mu cikin masu karantawa,
Fahimta da aiki da Alƙur'ani.
🤲 Ya Allah, Ka ɗaukaka mu da Alƙur'ani a duniya da Lahira.
Addinu Annasiha
Labari | A Karon Farko Ɗa da Uba Sun Kafa Babban Tarihi Na Zama Limamai a Masallacin Annabi (SAW).
Shaikh Ali bin Abdurrahman Al-Huzaify na daga cikin manyan limaman Masallacin Annabi a Madina, kuma ɗansa, Shaikh Ahmad Ali Al-Huzaify, shi ma an naɗa shi a matsayin limamin masallacin. Hakan ya sa suka zama ɗaya daga cikin fitattun iyalai da uba da ɗa suka yi hidimar jagorantar sallah a wannan masallaci mai alfarma.
Shaikh Ali Al-Huzaify ya shafe sama da shekaru arba'in yana jagorantar sallah da gabatar da huɗubobi a Masallacin Annabi, yayin da ɗansa Shaikh Ahmad Ali Al-Huzaify ya fara jagorantar sallah a matsayin baƙon limami kafin daga bisani a naɗa shi cikakken limami na masallacin.
Wannan wata babbar ni'ima ce da ke nuna yadda ilimi, tarbiyya da hidimar Alƙur'ani suka ci gaba daga uba zuwa ɗa a cikin wannan gida mai albarka.
Labari | Mutumin da ya kafa babban tarihi a duniya, sama da shekara (50) ana rubuta sunansa a jikin Kiswa - Rigar Ɗakin Ka'aba
Abdul Rahim Amin Bukhari fitaccen mai rubutun zane-zanen larabci (calligrapher) ne wanda aka haifa a birnin Makkah. Ya shiga masana'antar ƙera Kiswar Ka'aba yana ɗan shekara 15 kacal a shekara ta 1927.
A cikin fiye da shekaru 30 da ya yi yana aiki, ya ba da gudummawa wajen ƙera Kiswoyi 21 na Ka'aba da kuma ƙofofi uku na Ka'aba. Haka kuma, shi ne ya bunƙasa salon rubutun Thuluth da har yanzu ake amfani da shi wajen rubuce-rubucen da ke kan Kiswar Ka'aba mai tsarki.
Saboda gagarumar gudummawar da ya bayar wajen hidimar Kaaba, King Faisal ya karrama shi ta hanyar umartar a saka sunansa cikin Kiswar Ka'aba da zaren zinariya. Wannan suna nasa ya ci gaba da kasancewa a jikin Kiswar har zuwa yau, a matsayin abin tunawa da irin gudummawar da ya bayar ga wannan aiki mai daraja.
Mukhtar Alam Shaqdar is the master calligrapher responsible for inscribing the Qur’anic verses embroidered on the Kaaba’s Kiswa. Born in Saudi Arabia to a family of Bangladeshi heritage, he joined the Kiswa Manufacturing Complex in Makkah in 2002 after successfully passing a specialized calligraphy examination at Umm Al-Qura University.
While preserving the traditional Thuluth style that has adorned the Kiswa for generations, he enhanced the precision and elegance of its lettering and helped integrate modern digital tools into the calligraphic process. In recognition of his exceptional craftsmanship and contribution to this sacred tradition, he was later granted Saudi citizenship.
📸 Photo: Arab News