From me, my family, and my brothers and sisters united in love for our beloved Master, Prophet Muhammad (SAW), I wish you all a blessed and joyous Maulud Mubarak! 🖤
🌙Maulidin Annabi (SAW) ﷺ daga Senegal 🇸🇳
A lokacin karatun haihuwa daga littafin Shehu Ibrahim Inyass (RTA), Al-Faydhul Ahmady, an ba da dama a karanta tare har zuwa lokacin da za a mike tsaye, lokacin da Annabi (SAW) ﷺ yake zuwa. 🌹🤲🏽
Sai aka nutsu, aka bar mutum ɗaya ya karanta, sauran kuma suna amsawa da:
“Sallallahu Alaika Wa Ala Aalika Wa Sallam.” ﷺ❤️
Tunda a gaban Annabi (SAW) ﷺ. dole ayi nutsu wa ta musamman, numfashi ma a hankali akeyi.👍
Bayan an idar, aka yi addu’a saboda martabar Annabin da yake nan wurin a yanzu. 🤲🏽🌹
Allah Ya ƙara mana ƙaunar Manzon Allah (SAW) ﷺ, Ya karɓi wannan Maulidi, Ya albarkaci dukkan mahalarta. ❤️🌙🤲🏽
SHEIKH AL_HAJJ IBRAHIM NIASSE;
رَسُولٌ مِنَ الْمَوْلَى وَآدَمُ لَمْ يَكُنْ — وَيَبْقَى رَسُولًا دَائِمًا وَمُعَظَّمًا
A Messenger from the Lord, while Adam was not yet created — and he remains a Messenger eternally, greatly honored.
Allah ka lamunce mana ziyarar shugaba ﷺ, Allah kaita daukaka darajarmu, ka kiyaye mana mutunci da imanin mu, Allah kaita tsaya mana ka dafa mana, kai mana maganin abinda yafi karfinmu, ka wanzar da sutura da aminci a rayuwarmu, Allah ka lamunce mana cikawa da imani.
Maulanmu Shehu Ibrahim Inyass yana cewa:
Ya ku mutane, ku daina wasa da wargi, ku tsaya ku girmama Annabi Muhammad SAW.
in ba haka ba, za ku ga ni a koda yaushe ina tsayuwa da cikakken ƙarfi da tsanani wajen kare shi.
Ku cika duniya da salati da sallama ga Manzon Allah SAW kuma kada ku saurari mai zargin ku ko mai hana ku soyayyarsa.
Domin yawan nuna ƙauna gare Manzon Allah SAW itace madaidaiciyar hanya zuwa Aljanna.
Mafi girman cin amanar Shehu Tijâni da zaka yi shine ka zabi wadanda suke cigaba da rike da Almajiransa kuma daya daga cikin Khalifofinsa har yanzu.
#JusticeForKhalifa