Ready to ride the $SOON wave — @tonstationgames, you’ve outdone yourselves. Season 2 Airdrop by the millionssss$$. Going strong. https://t.co/XahiSMFLyr
Duk yanda mace take son ka, ba zai hana wataran ta taɓa ka ba.
Ko ta hanyar nuna soyayya ko kuma a matsayin gwaji domin taga tsananin son da kake mata, ko kuma kishi mai zafi akan ka.
Ka kula da irin macen da kake zama!
Ƙyauta itace ɗan aiken soyayya a tsakanin ma'aurata. Domin ƙyauta da tashin hankali ba sa zama guri ɗaya. Ƙyauta kala biyu ce a gidan aure:
1. Wadda ake iya taɓawa
2. Wadda ake iya ji a jiki, wato me ma'ana: Wannan tafi girma
Duk abinda Mace tayi maka; kayi ƙoƙari kada ya taɓa alfarmar Iyayenta, ƴaƴanta ko yan'uwanta. Ka bar shi tsakanin kai da ita kuma kar ka fasa aikata alherin da ka keyi ko kake son yi mata.
Idan mutum ya zama mai ƙaskantar da kai, da kauda kai, to kai kuma ka zama mai tunani da sanin ya kamata. Kar karinga yiwa mutum abinda bai dace da shi ba wanda ba zai iya yi maka magana ba saboda wasu dalilai; ko na girmamawa, ƙauna, ko makamantan su.
Ana so miji ya yawaita yabo ga matar sa domin mata suna son yabo. Yawaita yabon mace zai sa ta riga gyara laifukan ta domin ba ta so ace tayi laifin. Ka kai maƙura wajen:
1. Siffanta kyawun ta
2. Kyawun halayen ta
3. Kyawun tufafin ta
4. Kyawun ɗinki
5. Kyawun jikin ta.
Ana aure domin manufofi uku:
1) Ibaadah da Allah yace ayi.
2) Kare mutuncin kai daga aikata haram.
3) Samar da zuri'a da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama zai ji da ɗi da ita ranar gobe alƙiyama.
Haƙuri yana wanzuwa har ƙarshen rayuwa saboda shi ke riƙe aure. In har ya tafi; matsaloli zasu ringa samuwa kuma idan ba a kula sosai ba zai iya jawo rabuwar aure.
#marriedcouple#marriagetips#marriageadvice#northernhibiscus#opendiaries#marriagecounseling#northernnights
Abubuwa uku da ma'aurata ya kamata su shiga da shi gida; Kunya, Soyayya da Haƙuri.
Kunya tana tafi bayan sun kusanci juna musamman ace dukkanin su basu taɓa irin hakan ba.
Soyayya ta na tafiya bayan an haihu saboda dukan soyayyar ma'auratan tana komawa kan abinda aka haifa.